Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 16:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 16:26
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku fita, ku bar Babila Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji! Kada ku taɓa abin da aka hana, Ku kiyaye kanku da tsarki, Ku fita ku bar birnin.


Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata, Kada zunubanta su shafe ku, Kada bala'inta ya taɓa ku.


Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu, Ku keɓe, in ji Ubangiji, Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki, Ni kuwa in yi na'am da ku,


Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.


Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.


Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!


Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,


Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.


Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”


Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa.


Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ