Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku’ ”
Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!
Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.
Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa.