Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 15:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 15:29
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka'ida ɗaya ce domin taron jama'a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka'ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake.


“Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka'idodi na Idin Ƙetarewa. Ka'ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”


Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba'isra'ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa'an nan zai tsarkaka.


Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu.


Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”


ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan.


Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.


Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,


Wannan ka'ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.”


Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka.


“Sa'ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ