Ƙidaya 15:24 - Littafi Mai Tsarki24 idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra'ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra'ila, da raguna tasa'in da shida, da 'yan raguna saba'in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.