Ƙidaya 15:16 - Littafi Mai Tsarki16 Ka'ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka.