A faɗa wa dukan taron Isra'ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida.
Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.