Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’
Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”
Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa, suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”
kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’