Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 14:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Don me Ubangiji yana kawo mu wannan ƙasa yă bar mu kawai mu mutu da takobi? A kuma kwashe matanmu da ’ya’yanmu ganima. Ashe, bai fi mana mu koma Masar ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 14:3
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a ƙasar. Suna ta cin gaba da aikata mugunta, Ba su kuwa san ni ba.


Sau da yawa suka tayar masa a hamada. Sau da yawa suka sa shi yin ɓacin rai!


Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.


Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”


“Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”


Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?


Suka ce wa Musa, “Da ma mun mutu kamar yadda 'yan'uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji.


Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”


“Sa'an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma 'ya'yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta.


Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa, suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”


Suka ƙi yin biyayya, Suka manta da dukan abin da ka yi, Suka manta da al'ajaban da ka aikata. Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba, Don su koma cikin bauta a Masar. Amma kai Allah ne mai gafartawa, Kai mai alheri ne, mai ƙauna, Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.


kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’


“Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ