Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 14:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 14:29
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da su wa kuma ya yi fushi har shekara arba'in? Ashe, ba da waɗanda suka yi zunubi ba ne, waɗanda gawawwakinsu suka fādi a jeji?


Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra'ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sinai.


Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.


Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.


Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.


Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.


Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi, Bala'i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.


Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.


Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.


Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi, Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ