Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.
Musa ya ce wa Fir'auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama'arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?”