Ƙidaya 14:14 - Littafi Mai Tsarki14 Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Za su kuwa gaya wa mutanen wannan ƙasa. Sun riga sun ji cewa kai, ya Ubangiji, kana tare da waɗannan mutane, kuma cewa kai, ya Ubangiji, an gan ka fuska da fuska, cewa girgijenka ya tsaya bisansu, cewa kana tafiya a gabansu cikin ginshiƙin girgije da rana, da ginshiƙin wuta kuma da dare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.