Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”
Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.