Ƙidaya 13:29 - Littafi Mai Tsarki29 Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.