Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 13:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 13:28
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’


Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu.


Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”


Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak.


Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.


Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu,


Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, a can.


Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.


Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ