Ƙidaya 13:2 - Littafi Mai Tsarki2 “Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan'ana wadda nake ba Isra'ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 “Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu. Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza. Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu. Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan. Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru. Nabi ɗan Wofsi, daga kabilar Naftali. Geyuwel ɗan Maci, daga kabilar Gad.