9 Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su.
9 Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”
Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon.
Sa'ad da Allah ya gama magana da Ibrahim, sai ya tafi ya bar Ibrahim.
Ubangiji kuwa ya yi tafiyarsa, bayan ya gama magana da Ibrahim. Ibrahim kuwa ya koma gida.
Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.