9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.
9 Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.
Suka roƙa, sai aka ba su makware, Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.
Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, Maganata ta faɗo kamar raɓa, Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa, Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.
Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.