Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 11:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 11:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan.


Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba'in na Isra'ila.


“Sai ku naɗa alƙalai da shugabanni domin garuruwanku waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku bisa ga kabilanku. Sai su yi wa jama'a shari'a da adalci.


Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.


'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.


Sai kuma saba'in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!”


Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.


Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.


Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra'ila.


Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu.


Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama'a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba'in daga cikin jama'ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar.


Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa'an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama'a, da waɗansu manyan firistoci,


Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ