Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?
Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”
Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce, “Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja, Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.