Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 11:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 11:1
40 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”


Iliya kuwa ya ce musu, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka guda hamsin.” Wuta kuwa daga wurin Allah ta sauko daga sama ta cinye shugaban da mutanensa hamsin.


Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.


“Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata'awa.


Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.


Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama'ar Isra'ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.”


Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.


Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Wuta ta sauko bisa magoya bayansu, Ta ƙone mugayen mutanen nan.


Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su, Ya aukar wa jama'arsa da wuta, Fushinsa ya haɓaka a kansu,


Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”


Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.


Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.


Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”


Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”


Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sinai, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki.


Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi.


Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.


Duwatsu sukan girgiza a gabansa, Tuddai kuma su narke. Duniya ta murtsuke a gabansa, Da dukan mazauna a cikinta.


Don me ɗan adam Zai yi gunaguni a kan hukuncin zunubansa?


Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.


Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.


Dukan Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji.


dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,


“Har yaushe wannan mugun taron jama'a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra'ilawa suka yi a kaina.


Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku.


Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”


Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra'ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”


Aka karkashe samari a cikin yaƙi, 'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.


Allah da yake hasken Isra'ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.


Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.


Annoba tana tafe a gabansa, Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.


Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ