Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 10:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 10:14
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Rana Kabila Shugaba Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.


“Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka.


Sa'ad da kuka yi busar faɗakarwa, waɗanda suke zaune a gabashin zangon za su tashi.


Shugaban rundunar kabilar mutanen Issaka Netanel ne, ɗan Zuwar.


A lokacin da Isra'ila yake zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari. 'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne.


'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.


Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa. Kabila Shugaban Kabila Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Naftali Ahira ɗan Enan


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ