13 Suka fara tafiyarsu bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa.
13 Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.
“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.
Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.
Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.
Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.