Ƙidaya 10:12 - Littafi Mai Tsarki12 Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu. Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza. Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu. Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan. Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru. Nabi ɗan Wofsi, daga kabilar Naftali. Geyuwel ɗan Maci, daga kabilar Gad.