Ƙidaya 10:10 - Littafi Mai Tsarki10 A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.