Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600).
Saboda haka Isra'ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.