Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 1:18 - Littafi Mai Tsarki

18 suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 1:18
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra'ila ne.


Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada.


Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu.


Amma wannan, wanda ma ba a asalin Lawi yake ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai.


A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,


Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu,


Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ