Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 1:1
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”


Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.


Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sinai a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce,


Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.


Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce


A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa.


“A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.


A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.


suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,


Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina'i, sai suka yi zango gaban dutsen.


Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi.


A shekara ta arba'in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra'ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu.


Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’


Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ