“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.
Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.
Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku.