3 A ƙofofin shiga birni, tana kira,
3 kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,
A sa'ad da nakan tafi kofar birni, In shirya wurin zamana a dandali,
“Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama'a duk maganar wannan rai.”
Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.
Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’
“Ina roƙonku, ya ku, 'yan adam, Ina kiran kowane mutum da yake a duniya.
Tana kira da ƙarfi a ƙofofin birni, a duk inda mutane suke tattaruwa.