6 Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina,
6 A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi, Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce, “Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa? Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?”
Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.
Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.
Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.
Ƙaunataccena kamar barewa yake, Kamar sagarin kishimi. Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu. Yana leƙe ta tagogi, Yana kallona ta cikin asabari.