4 Ka mai da hikima 'yar'uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka.
4 Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
Da ma a ce kai ɗan'uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya, Da in na gamu da kai a titi, Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.
Zan ce kabari shi ne mahaifina, Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da 'yan'uwana mata.
Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka.
Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.