Albarka tā tabbata ga mai karanta maganar nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma suke kiyaye abin da yake a rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.
Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”
Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.
Za ku zama la'anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba.