2 Maganganunka sun taɓa kama ka, ko alkawaranka sun taɓa zamar maka tarko?
2 in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
Sa'ad da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce, da ita ake kama shi.
Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.
Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu.
Ɗana, ka taɓa yin alkawari ka ɗaukar wa wani lamuni?
To, ɗana, kana cikin ikon wannan mutum, amma ga yadda za ka yi ka fita, sheƙa zuwa wurinsa, ka roƙe shi ya sake ka.