9 Za ta zamar maka rawanin daraja.”
9 Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau.
Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.
Rana tana zuwa da Ubangiji Mai Runduna zai zama kamar rawanin furanni mai daraja ga jama'arsa da suka ragu.
Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.
Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.
sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.
Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki.
Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai.
Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.
Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.