Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa.
Sarki Dawuda fa ya yi magana da dukan taron, ya ce, “Ga shi, ɗana Sulemanu, wanda Allah ya zaɓa, shi dai saurayi ne tukuna, bai gogu da duniya ba tukuna, aikin kuwa babba ne, gama Haikali ba na mutum ba ne, amma na Ubangiji Allah ne.
“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.