2 Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata.
2 gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai.
Hikima za ta ƙara shekarunka.
Zan ba su tsawon rai lada, Hakika kuwa zan cece su.”
Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Ya kuma sa ka ka ga jikokinka! Salama ta kasance ga Isra'ila!
Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya, Ba wani abin da zai sa su fāɗi.
Ka yi tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai ƙare ba.
Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.
To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo, Da yawan kwanaki.
Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.
Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.
don kwanakinku da kwanakin 'ya'yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya.
Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”
Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.
“Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu.
mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.