Wane mu mu daidaita kanmu, ko mu gwada kanmu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe, waɗannan mutane masu auna kansu da juna, suna kuma neman bambanci a tsakaninsu da juna, ba su da basira.
Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.