9 Karin magana a bakin wawa kamar sukar ƙaya ce a hannun mai maye.
9 Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.
Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”
Wanda ya yabi wawa yana kama da wanda ya ɗaura dutse a majajjawa.
Wanda ya ɗauki wawa aiki yana cutar duk wanda aikin ya shafa.