3 An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi.
3 Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.
gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.
Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai.
kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya, Ta wurin hikimarsa ya kafa ta, Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗa sammai.
Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.’ Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka.