Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Karin Magana 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Karin Magana 2:4
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”


Kowa ya bar gidaje, ko 'yan'uwa mata, ko 'yan'uwa maza, ko uwa, ko uba, ko 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.


Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.


Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa, Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.


Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.


mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.


Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu.


Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya, Fiye da zinariya tsantsa.


Dokar da ka yi Muhimmiya ce a gare ni, Fiye da dukan dukiyar duniya.


Ina murna da bin umarnanka, Fiye da samun dukiya mai yawa.


Abin da ake so ne fiye da zinariya, I, fiye da tatacciyar zinariya ma, Sun fi zuma zaƙi, I, fiye da tatacciyar zuma ma.


Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.


Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”


Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ