“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
Na ga wannan duka a sa'ad da nake tunani a kan abubuwan da ake yi a duniyan nan, duniyar da waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.
To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.