Karin Magana 1:9 - Littafi Mai Tsarki9 Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”