Za a haifa maka ɗa, zai zama mutumin salama. Zan kuwa ba shi zaman lafiya da abokan gāba da suke kewaye da shi, gama za a ce da shi Sulemanu, wato salama. Zan kawo wa Isra'ila salama, da natsuwa a zamaninsa.
Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.
Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.
Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.