Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.
A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.
Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.
Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
Mulkin Isra'ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.