Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 8:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko'ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 8:21
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ko'ina a ƙasar jama'a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har 'ya'yansu ma suke ci!


Waɗansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa'an nan su sa wa Ubangiji laifi.


A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.


Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”


Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?”


Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”


Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”


A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar.


“Kada ku saɓi Allah, kada kuma ku zagi mai mulkin jama'arku.


Yana magana da su ke nan, sai sarki ya iso, ya ce, “Wannan masifa daga wurin Ubangiji ta fito, don me zan ƙara jiran Ubangiji kuma?”


Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan.


A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”


Dā attajiri ne, amma yanzu ya talauce, Kusa da shi bala'i na tsaye yana jiransa.


Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Ubangiji zai zama makiyayin jama'arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.


Masifa riɓi biyu ta auko miki, Yaƙi ya lalatar da ƙasarki, Mutanenki suka tagayyara da yunwa.


Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu.


Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ