Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.
Ubangiji zai zama makiyayin jama'arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.