Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 7:11 - Littafi Mai Tsarki

11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 7:11
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.


Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”


Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu.


“Sa'an nan sai ka fasa tulun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai,


Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa'an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama'a, da waɗansu manyan firistoci,


Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”


“Idan Fir'auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al'ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir'auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”


Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce,


Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”


Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu, Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa. Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada, Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”


Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.


Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ