Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi, Suna yi wa kansu gumaka na zubi, Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu, Dukansu aikin hannu ne. Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!” Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.
Lokaci zai yi sa'ad da jama'ar Isra'ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al'ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra'ila.
Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.