Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa. Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna. Yanzu za ki ƙara samun 'ya'ya fiye da na Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!
Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.
Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu.