Ishaya 66:5 - Littafi Mai Tsarki5 Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |